Shugaba Hassan Rauhani ya ci gaba da cewa; Fagagen da kasashen biyu za su iya aiki akansu sun hada da noma, ilimi, al'adu da masana'antu.
Rauhani ya ci gaba da cewa al'ummar Zimbabwe, al'umma ce mai gwagwarmaya, kuma tamkar al'ummar Iran suna cin gashin kansu da 'yanci, don haka su ke da alaka da juna tun farkon cin nasarar juyin musulunci.
Robert Mubage dai ya iso Iran ne domin halartar bikin rantsar da shugaban Hassan Rauhani a zango na biyu na mulkinsa.288